logo

HAUSA

Wang Yi: Jawabin Xi a taron FOCAC ya bayyana alkiblar dangantakar Sin da Afrika

2021-12-01 09:46:04 CRI

Wang Yi: Jawabin Xi a taron FOCAC ya bayyana alkiblar dangantakar Sin da Afrika_fororder_王毅

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya bayyana jawabin da shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar yayin taron ministoci na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC karo na 8, a matsayin mai muhimmanci da ya bayyana hanyoyin raya dangantakar bangarorin biyu.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron, Wang Yi ya bayyana shi a matsayin katafaren taro na aminci tsakanin Sin da Afrika, tun bayan irinsa da aka yi a 2018, haka kuma babban taron diflomasiyya da Sin ta shirya tun bayan barkewar COVID-19, kuma wanda ta yi da ‘yan uwanta kasashe masu tasowa.

A cewarsa, yayin wannan taro, shugaba Xi da shugabanni kasashen Afrika, sun tattauna kan tsarukan raya Sin da Afrika da makomar dangantakarsu, wadda ke da muhimmanci ga zurfafa hadin gwiwa da goyon baya tsakanin kasashe masu tasowa da hadin kan duniya wajen yaki da cutar COVID-19, ta yadda zaman duniya da tsarin shugabanci, za su kasance bisa daidaito da adalci.

Har ila yau, Wang Yi ya ce, kasar Sin za ta bayar da sabuwar gudunmuwa ga hadin gwiwarta da Afrika wajen shawo kan annobar COVID-19, da karfafa hadin gwiwa da goyon bayan juna da samun ci gaba na bai daya da kokarin gina al’umma mai makoma ta bai daya ta Sin da Afrika a sabon zamani. (Fa’iza Mustapha)