logo

HAUSA

WHO: Bai Kamata A Yi Riga Malam Masallaci Kan Sabon Nau’in Omicron Ba

2021-12-01 19:02:44 CRI

WHO: Bai Kamata A Yi Riga Malam Masallaci Kan Sabon Nau’in Omicron Ba_fororder_1201-01

A ’yan kwanakin nan ne dai, kasar Afirka ta kudu ta sanar da bullar wani sabon nau’in annobar COVID-19 da hukumar lafiya ta duniya kirar Omicron a cikin kasarta. Sai dai sanar da bullar sabon nau’in kwayar cutar ke da wuya, sai wasu kasashe suka sanar da haranta shigar fasinjoji daga dukkan kasashen dake kudancin Afirka baki daya shiga cikin kasashensu. Ya kamata irin wadannan kasashe dake daukar matakan harancin shiga kasashen nasu su fahinci cewa, ba su ne suka kar zomon ba…

Amma hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce kawo yanzu, ba a kai ga tantance ko nau’in Omicron na cutar COVID-19 ya fi saurin yaduwa da illa ga lafiyar bil adama ba. Kaza lika babu tabbas game da tasirin nau’in cutar sama da sauran nau’o’in kamar na Delta. Don haka daukar irin wannan mataki da wasu kasashe suka yi,ana iya cewa ba zai haifar da da mai ido ba.

Haka kuma hukumar ta ce, ba a kai ga tabbatar da ko nau’in na Omicron na haifar da wasu alamun ciwo na daban sabanin na sauran nau’o’in cutar COVID-19 ba, saboda gane hakan kan dauki kwanaki ko ma makwanni. A saboda haka, daukar duk wani irin mataki da ya saba na kimiya, tamkar riga malam masallaci ne.

Shi ma, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce hanya daya tilo ta ganin bayan annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar dukkanin sassan duniya, ita ce aiwatar da cikakken shirin rigakafi na bai daya.

Bayanan masana kimiya sun nuna cewa, zai dauki lokaci kafin a tantance yanayin tasirin wannan nau’i na cutar COVID-19, duk da cewa adadin masu harbuwa da ita na karuwa, ana kuma kwantar da masu kamuwa da ita a Afirka ta kudu.

Kamar kullum a wannan karon ma hukumar WHO ta tabbatar da cewa, dukkanin nau’o’in COVID-19, ciki har da nau’in Delta wanda shi ne mafi yaduwa a duniya na iya haifar da ciwo mai tsanani ko asarar rayuka, musamman ga rukunin mutane masu raunin, don haka daukar matakan kandagarki shi ne mafi tasiri ba wai hana jama’ar wasu kasashe ko yankuna shiga wata kasa ba kwata-kwata.

Kasar Sin dai ta yaba da yadda kasar Afirka ta Kudu ta yi musayar bayanai a kan lokaci kan sabon nau'in Omicron na annobar COVID-19 da aka gano, za kuma ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya, gami da kasashen kudancin Afirka, domin ganin an yaki cutar ta hanyar kimiyya, sannan kasashe su goyi bayan jagorancin hukumar lafiya ta duniya.

Masu fashin baki sun bayyana cewa, matakai na kimiya sune hanyoyi mafi dacewa na magance wannan annoba dake ci gaba da yiwa duniya daurin huhun goro. (Ibrahim Yaya)