logo

HAUSA

Mutane 11 sun rasu 252 sun tsere daga gidan yarin Jos na jihar Plateau

2021-11-30 09:50:44 CRI

Mutane 11 sun rasu 252 sun tsere daga gidan yarin Jos na jihar Plateau_fororder_211130-prison-Saminu

A kalla mutane 11 ne suka rasu, kuma wasu firsinoni 252 suka arce daga gidan yarin birnin Jos fadar mulkin jihar Plateau dake yankin tsakiyar Najeriya.

Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, bayan da wasu gungun ’yan bindiga suka bude wuta kan jami’an tsaron gidan yarin, kana suka kutsa kai cikin sa tare da kubutar da wadanda ake tsare da su.

Da yake karin haske game da hakan, kakakin hukumar dake kula da gidajen yarin Najeriya Francis Enobore, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an harbe daya daga masu gadin gidan yarin, an kuma harbi wani na daban a hannu, yayin da kuma firsinoni 9 suka rasa rayukansu, baya ga wasu 6 da suka jikkata.

Bugu da kari, sanarwar ta ce an harbe daya daga cikin maharan, yayin da sauran suka tsere tare da firsinoni da dama kafin zuwan karin jami’an tsaro.

Jami’in ya ce bayan dauki ba dadin, jami’an tsaro sun sake cafke 10 daga cikin firsinonin da suka yi kokarin guduwa, yayin da kuma ake ci gaba da neman 252.  (Saminu Alhassan)