logo

HAUSA

Nijeriya ta shiryawa tunkarar nau’in cutar COVID-19 na Omicron

2021-11-30 10:07:00 CRI

Nijeriya ta shiryawa tunkarar nau’in cutar COVID-19 na Omicron_fororder_211130-cuta-Faeza1

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya, ta ce hukumomin lafiya a kasar, na bibiyar yanayin barkewar sabon nau’in cutar COVID-19 na Omicron da tasirinsa.

Shugaban cibiyar, Ifedayo Adetifa, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, kasar ta yammacin Afrika ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tunkarar nau’in na Omicron ba. Yana mai cewa, har yanzu ba a gano shi ba a kasar. Sai dai, ya gargadi al’umma da su kaucewa ziyartar kasashen da aka samu rahoton bullar cutar.

Ya ce bisa la’akari da yuwawar saurin yaduwar nau’in na Omicron da bullarta dake da alaka da bazuwarta a tsakanin al’umma, cibiyar ta bukaci ’yan Nijeriya su tabbatar da kiyaye matakan lafiya da aka gindaya.

Ya ce biyo bayan yadda yanayin nau’i cutar ke sauyawa da kuma karuwar masu kamuwa da ita da aka gani a kasar Afrika ta Kudu, ana ganin wannan nau’in a matsayin mai saurin yaduwa, haka kuma mai yuwa ya kara barazanar sake kamuwa da cutar, idan aka kwatanta da sauran nau’o’i.  (Fa’iza Mustapha)