logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Najeriya: FOCAC na kokarin gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka

2021-11-29 10:11:39 CRI

Jakadan Sin dake Najeriya: FOCAC na kokarin gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka_fororder_FOCAC

Jakadan kasar Sin a tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya wallafa wani sharhi mai taken “Dandalin FOCAC yana kokarin gina kyakkyawar makomar kasar Sin da kasashen Afirka” a wasu muhimman kafofin watsa labarai na Najeriya, kamar su jaridar “Sun”, da “Blueprint” tsakanin ranar 26 zuwa 28 ga wannan wata. Cikin sharhin na sa, jakada Cui ya bayyana cewa, za a kira taron ministocin dandalin taron hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC karo na takwas a Dakar, fadar mulkin kasar Senegal tsakanin ranar 29 zuwa 30 ga wata, inda ministocin kasar Sin da Najeriya, da ma hukumar AU za su sake taruwa wuri daya, domin tattauna kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za su tsara sabon salon hadin gwiwa tsakanin sassan biyu a nan gaba.

Babban taken taron shi ne “Zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka domin ingiza dauwamamman ci gaba, tare kuma da gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamanin da ake ciki”. Ana sa ran cewa, taron zai taka sabuwar rawa wajen ciyar da huldar abokantaka dake tsakanin Sin da Afirka gaba daga dukkanin fannoni, da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da kuma sa kaimi kan zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ci gaba, da wadata a fadin duniya, bayan da aka kawo karshen yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19. (Jamila)