FOCAC 2021: Tsokacin Masu Ruwa Da Tsaki Game Da Alfanun Hadin Gwiwar Sin Da Afrika
2021-11-29 17:25:30 CRI
Yayin da shirye shirye suka kammala don gudanar da taron ministoci na dandanlin hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika wato FOCAC, wanda ake sa ran gudanarwa tsakanin ranakun 29 zuwa 30 ga watan nan na Nuwamba a Dakar, babban birnin kasar Senegal, masu ruwa da tsaki na bangarori Sin da Afrika sun yi ta tofa albarkacin bakinsu game da alfanu da kuma tasirin da taron ministoci zai haifar ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika. Shugabanni da dama na bangarorin biyu sun bayyana ra’ayoyinsu game da muhimmancin hadin gwiwar Sin da Afrika karkashin dandalin FOCAC. Alal misali, a karshen wannan mako, wasu daga cikin jaridun Najeriya da suka hada da jaridar The Sun, da kuma Blueprint, sun wallafa tsokacin da jakadan kasar Sin a tarayyar Najeriya Cui Jianchun ya yi, mai taken “Dandalin FOCAC yana kokarin gina kyakkyawar makomar kasar Sin da kasashen Afirka.” A cikin sharhin nasa, jakada Cui ya bayyana cewa, taron kolin FOCAC karo na takwas da za a gudanar a Dakar, fadar mulkin kasar Senegal tsakanin 29 zuwa 30 ga wata, inda ministocin kasar Sin da Najeriya, da ma hukumar AU za su sake taruwa wuri guda, domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za su tsara sabon salon hadin gwiwa tsakanin sassan biyu a nan gaba.
Babban taken taron shi ne “Zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka domin ingiza dauwamammen ci gaba, tare kuma da gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamanin da muke ciki”. Ana sa ran taron zai taka sabuwar rawa wajen ciyar da huldar abokantaka dake tsakanin Sin da Afirka gaba daga dukkan fannoni, da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da kuma sa kaimi kan zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ci gaba, da wadata a fadin duniya, bayan da aka kawo karshen yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19. A nata bangaren, kwamishiniya mai kula da fannin kiwon lafiya, da ayyukan jinkai da kyautata jin dadin alumma ta kungiyar tarayyar Afrika AU, Amira Elfadil, ta bayyana yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua gabanin fara taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC, karo na takwas, ta ce gwamnatin kasar Sin ta cancanci yabo da dukkan masu ruwa da tsaki bisa jajircewarsu wajen gina kyakkyawar dangantaka mai karfi tsakanin Sin da Afrika. Shi ma, tsohon shugaban kasar Najeriya, kana shugaban majalisar tattaunawa na tsoffin shugabannin kasashen duniya wato InterAction, Olusegun Obasanjo, ya bayyana a tattaunawarsa da wakilin gidan talabijin na CGTN, a karshen mako cewa, yana fatan taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika FOCAC karo na takwas zai tattauna abubuwan da Afrika ke bukata a yayin da ta samu taimakon kasar Sin, domin nahiyar ta samu zarafin tsayawa da kafafunta, wajen inganta fannin kiwon lafiya don dakile annobar COVID-19. Ya kara da cewa, inganta kyakkyawar huldar dake tsakanin Sin da Afrika zai samar da moriya ga dukkan bangarorin biyu. Hakika, kamar yadda masu hikimar magana ke cewa, “alamun karfi yana ga mai kiba,” ana fatan taron ministoci na FOCAC na wannan karo zai kara ingizawa da kuma karfafa huldar ciniki, da tattalin arziki, gami da yaki da annobar COVID-19 tsakanin Sin da kasashen Afrika. (Ahmad Fagam)