logo

HAUSA

An gudanar da taron yin musayar ra’ayoyi kan bidiyon “Jihar Xinjiang wuri ne mai kyau” a Urumqi

2021-11-28 17:31:12 CRI

An gudanar da taron yin musayar ra’ayoyi kan bidiyon “Jihar Xinjiang wuri ne mai kyau” a Urumqi_fororder_1128-1

A ranar 26 ga wata da yamma, an gudanar da taron yin musayar ra’ayoyi kan bidiyon “Jihar Xinjiang, wuri ne mai kyau” a tsakanin wakilan bangarorin masana’antu da kasuwanni na kasashen waje dake kasar Sin a birnin Urumqi na jihar Xinjiang.

Zaunannen mamban kwamitin jam’iyyar kwaminis ta Sin na jihar Xinjiang kuma shugaban kungiyar kwadago ta jihar Ilzat Ahmatjan ya yi bayani game da yanayin bunkasuwar tattalin arzikin jihar, da manufofin jihar na bude kofa ga kasashen waje, da kyautata zaman rayuwar jama’ar jihar da sauransu. Ya bayyana cewa, a cikin rubu’i uku da suka gabata a bana, yawan GDPn jihar Xinjiang ya karu da kashi 8.8 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Yawan kudin cinikin waje na shigi da fici na jihar Xinjiang na lokacin ya kai dalar Amurka biliyan 17.115, wanda ya karu da kashi 11.6 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. An cimma ayyukan zuba jarin waje ga jihar guda 4819. Ya zuwa karshen watan Oktoba na shekarar bana, yawan jiragen kasa da suka ratsa jihar Xinjiang zuwa nahiyar Turai ya kai dubu 33, wanda ya zarce rabin jimillar jiragen kasan da suka yi tafiya a kasar Sin baki daya. (Zainab)