logo

HAUSA

Cibiyar Africa CDC ta bukaci a karfafa matakan kandagarkin COVID-19 yayin da aka samu bullar sabon nau’in cutar

2021-11-27 16:58:42 CRI

Cibiyar Africa CDC ta bukaci a karfafa matakan kandagarkin COVID-19 yayin da aka samu bullar sabon nau’in cutar_fororder_1352167086290108427

Cibiyar kandagarki da yaki da yaduwar cututtuka ta Afrika wato Africa CDC, ta bukaci hukumomin lafiya a Afrika, su matse kaimi wajen daukar matakan kandagarkin COVID-19 yayin da wani sabon nau’in cutar ya bullo.

Africa CDC ta yi kiran ne rana guda, bayan cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afrika ta Kudu, ta sanar da gano sabon nau’in kwayar cutar COVID-19, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana a matsayin abun damuwa.

Cibiyar ta yi kira ga kasashen nahiyar su gaggauta yi wa al’umma allurar riga kafin cutar domin dakile yaduwarta, tana mai cewa, kawo yanzu, riga kafi ne muhimmiyar hanyar kare tsanantar cutar da mace-macen da take haifarwa.

Da kuma safiyar yau Asabar ne, Kungiyar kula da cinikayya ta duniya WTO, ta sanar da dage taro karo na 12 na ministocin kungiyar, saboda bullar sabon nau’in cutar a kasashe da dama.

A baya, an shirya taron zai gudana ne daga ranar Talata zuwa Juma’a a Geneva. Zuwa yanzu dai, ba a saka ranar da za a gudanar da taron ba. (Fa’iza Mustapha)