logo

HAUSA

Babu Wani Karfi Da Zai Iya Girgiza Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

2021-11-27 16:26:53 cri

Babu Wani Karfi Da Zai Iya Girgiza Hadin Gwiwar Sin Da Afirka_fororder_微信图片_20211127151509

“‘Rijiyar kasar Sin’ kyauta ce ta ceton rayuwa.” Sakamakon rashin tsaftataccen ruwan sha da aka dade ana fama da shi a kauyen Lumene na kasar Zimbabwe, mazauna kauyen da dama sun kamu da cutar kwalara da sauran cututtuka. A watan Agustan bana, wata rijiya da aka hako da taimakon gwamnatin kasar Sin, ta kyautata yanayin tsaftar muhalli, hakan ya sa mazauna kauyen ba su kara kamuwa da cututtuka sakamakon ruwa maras tsafta ba. Tun daga shekarar 2012 zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta taimaka wa kasar Zimbabwe hako rijiyoyi 1,000, wadanda suka amfanawa sama da mutane 400,000 na kasar.

Kananan rijiyoyi sun nuna dadadden zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka. Wata shahararriyar hukumar binciken ra’ayoyin jama’a ta Afirka, ta fitar da wani rahoto a baya-bayan nan, wanda ke cewa, kasar Sin tana kan gaba wajen yin tasiri a nahiyar Afirka.

A ranar 26 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani mai suna "Hadin gwiwar Sin da Afirka a sabon zamani", wadda ta waiwayi nasarorin da aka samu a hadin gwiwar Sin da Afirka.

Ga misali, a yayin da kasar Sin ke fama da annobar COVID-19, wasu kasashen Afirka, duk da ba su da wadata, sun ba da gudummawar kudi da kayayyaki ga kasar Sin. Bayan bullar annobar a Afirka, kasar Sin ta yi gaggawar taimakawa, inda zuwa yanzu, ta samar da alluran rigakafi kusan miliyan 200 ga kasashen Afirka, tare da sanar da rage basussuka marasa ruwa ga kasashe 15 na Afirka kafin karshen shekarar 2020.

Bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", kasar Sin tana kara taimakawa kasashen Afirka wajen inganta ababen more rayuwa. A sa'i daya kuma, tana taimakawa kasashen Afirka wajen horar da kwararru a fannonin kimiyya da fasaha da gudanar da hadin gwiwa a wasu sabbin fannoni.

Nan da 'yan kwanaki masu zuwa, za a gudanar da taron ministoci na sabon zagaye na dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a kasar Senegal, inda kasar Sin za ta sanar da sabbin manyan matakan hadin gwiwa da kasashen Afirka nan da shekaru uku masu zuwa, wadanda ko shakka babu za su kara samar da moriya ga jama'ar bangarorin biyu. (Mai fassara: Bilkisu)