logo

HAUSA

An kammala mataki na 1 na aikin gina babban hedkwatar cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka karkashin taimakon gwamnatin kasar Sin.

2021-11-27 16:35:35 cri

Babu Wani Karfi Da Zai Iya Girgiza Hadin Gwiwar Sin Da Afirka_fororder_20211127022848997

An kammala aikin gina mataki na 1, na kololuwar ginin babban hedkwatar cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka da ake yi karkashin taimakon gwamnatin kasar Sin, a jiya Jumma’a a yankin kudancin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha,

Wannan aikin wani muhimmin sashe ne dake cikin "Aikin Lafiya" bisa ajandar dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, haka kuma wani muhimmin gini ne na zumunci da hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, bayan ginin hedkwatar Tarayyar Afirka.

Babu Wani Karfi Da Zai Iya Girgiza Hadin Gwiwar Sin Da Afirka_fororder_20211127022849018

A yayin bikin kammala aikin, jakadan kasar Sin a tarayyar Afirka Liu Yuxi, ya bayyana cewa, Sin da kasashen Afirka suna taimaka wa juna, da yin kokari kafada da kafada, domin tinkarar annobar COVID-19, da kuma kara sa kaimi ga zurfafa dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata. Ya ce kasar Sin ma tana son ci gaba da hada gwiwa da kungiyar tarayyar Afirka don cimma ra’ayin bai daya, da karfafa hadin kai, da zummar karfafa gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka.

A madadin shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, kwamishiniyar kula da harkokin al’umma ta kungiyar Amira Elfadil, ta godewa kasar Sin bisa taimakon da ta yi. Har ila yau, ta bayyana cewa, aikin cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka, wani muhimmin ginshiki ne ga al'ummar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiya. (Mai fassara: Bilkisu)