logo

HAUSA

Amurka ta sake shaidawa duniya yunkurinta na siyasa

2021-11-26 10:52:56 CRI

Amurka ta sake shaidawa duniya yunkurinta na siyasa_fororder_1126-02

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta sanar a kwanakin baya cewa, za ta gayyaci hukumar yankin Taiwan data halarci taron da take kira wai "Taron kolin dimokuradiyya ". Amurka tana son yin amfani da demokuradiyya don nuna goyon baya ga raba yankin Taiwan daga babban yankin kasar Sin, matakin na kasar Amurka tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gida na kasar Sin, ya kuma saba wa manufar Sin daya tak a duniya, da yunkurin haifar da baraka, da kawo babbar illa ga martabar demokuradiyya. A don haka, Sin tana adawa da wannan mataki.

Manufar kasar Sin daya tak, ka’ida ce da kasa da kasa suka amince da ita. A matsayinsa na wani bangare na kasar Sin, yankin Taiwan ba shi da ikon zama wata kasa bisa dokokin kasa da kasa ba. Kasar Amurka tana son yin amfani da maganar demokuradiyya, don kaucewa hukuncin da aka yanke wa masu janyo barakar kasa bisa dokokin kasa da kasa, da nuna goyon baya ga ‘yan aware na yankin Taiwan, kuma hakan zai kara shaidawa duniya cewa, batun demokuradiyya, wata hanya ce da kasar Amurka ta ke amfani da ita wajen ta da rikice-rikice, da danna sauran kasashe, da kuma neman biyan bukatunta na siyasa.

Ana sa ran cewa, ko da kasar Amurka ta kira "Taron kolin dimokuradiyya ", ba za ta iya bayyana ma’anar demokuradiyya ba, za kuma ta shaidawa duniya yanayin demokuradiyya na kasar Amurka dake yin amfani da munafunci da ma’auni biyu, da kuma yunkurinta na son kai. (Zainab)