logo

HAUSA

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na FOCAC

2021-11-26 20:13:03 cri

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na FOCAC_fororder_f636afc379310a551b0eaed3ba4543a9822610ea

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron ministoci karo na 8, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) ta kafar bidiyo a ranar 29 ga watan Nuwamban nan, tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Game da haka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba yi a yau Jumma’a, cewa wannan gaggarumin biki ne da kasar Sin tare da kasashen Afirka za su shirya, bisa lokacin da aka tsaida bayan kawar da wahalhalu.

Zhao ya kara da cewa, hakan ya biyo bayan taron kolin Johannesburg na FOCAC na shekarar 2015, da taron kolin Beijing na FOCACn na shekarar 2018, da taron koli na musamman na yaki da annobar COVID-19 na Sin da Afirka na shekarar 2020, inda shugaba Xi Jinping, ya kara tsara alkiblar raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a nan gaba, tare da shugabannin kasashen Afirka. Kaza lika taron wani babban matakin diplomasiyya ne da kasar Sin za ta aiwatar game da kasashe masu tasowa, kana zai zama wani gaggarumin biki da babban iyalin Sin da Afirka za su shirya, bisa lokacin da aka tsara bayan shawo kan matsaloli aukuwar annobar COVID-19.

Baya ga haka, Zhao ya bayyana cewa, bayan bikin bude taron, ministocin harkokin waje, ko wakilansu, da ministocin dake kula da harkokin hadin kai da ketare a fannin tattalin arziki na kasashe mambobi 54 na dandalin, da kuma wakilan kungiyar Tarayyar Afirka, za su gudanar da wani taro don tantance halin tabbatar da nasarorin da aka cimma a gun taron kolin Beijing, da yadda ake yin hadin kai tsakanin Sin da Afirka wajen yaki da annobar, kana da tsara alkiblar raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu a cikin shekaru uku ko fiye masu zuwa. Za kuma a yi amfani da ingantattun nasarorin hadin gwiwa da aka cimma, don kara samar da alheri ga jama’ar Sin da kasashen Afirka, tare kuma da inganta raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani. (Mai fassara: Bilkisu)