logo

HAUSA

Xi Jinping zai halarci bikin bude taron ministocin dandalin FOCAC karo na 8

2021-11-26 10:48:56 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi.

Ya zuwa yanzu, dandalin FOCAC ya kunshi membobi 55 da suka hada da kasar Sin, da kasashen Afirka 53 wadanda suka kulla dangantakar diplomasiyya da Sin, da kuma na hukumar gudanarwar kungiyar AU. An gudanar da taron kolin dandalin sau 3, da taron ministoci sau 7, inda aka tsara takardun hadin gwiwa da dama masu muhimmanci, da sa kaimi ga daukar matakan nuna goyon baya ga raya kasashen Afirka, da zurfafa hadin gwiwa da sada zumunci a tsakanin bangarorin Sin da Afirka. (Zainab)