logo

HAUSA

Ministan harkokin waje da na cinikayyar kasar Sin za su halarci taron FOCAC dake tafe

2021-11-26 20:44:11 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da ministan cinikayyar kasar Wang Wentao, za su halarci taron ministoci karo na 8, na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, wanda zai gudana a birnin Dakar na kasar Senegal, tsakanin ranekun 29 zuwa 30 ga watan nan na Nuwamba.

Zhao ya kara da cewa, kafin halartar taron, Wang Yi zai gudanar da ziyarar aiki a Senegal, bisa gayyatar da takwararsa ta kasar Aissata Tall Sall ta yi masa.  (Saminu)