Sin na aiwatar da salon dimokaradiyya mafi dacewa da ci gaban al’umma
2021-11-25 18:51:10 CRI
Har kullum kasashen yammacin duniya na ambatar kalmar dimokaradiyya, domin nunawa duniya irin nasarorin da suka cimma a fannin kare hakkokin bil adama, da baiwa al’umma damar cimma burikan su na rayuwa, to sai dai kuma a hannu guda, da yawa daga kasashen yammacin duniya kan fake da wannan kalma wajen sukar sauran kasashe, suna masu zargin su da kin bin dimokaradiyya yadda ya kamata.
Ko shakka babu, dimokaradiyya ta bambanta daga kasa zuwa kasa gwargwadon yanayin kasashen, kuma ko wace kasa na da salonta na aiwatar da dimokaradiyya. Duk da cewa kafofin watsa labaran yamma suna yawan ambaton wannan kalma ta dimokaradiyya, da ’yancin dan Adam ba tare da la’akari da cikakkiyar ma’anar su ba, a hannu guda al’ummar Sinawa sun zabi maida hankali ga bunkasa ci gaban tattalin arziki, a matsayin jigon dimokaradiyya, domin kuwa in har babu ci gaba, kuma ba a kawar da talauci ba, dimokaradiyya ba za ta yi amfani ba, kuma mutane ba za su samu wani ’yanci mai ma’ana ba.
Wannan ne ma ya sa sau da dama, kafofin yamma ke sukar kasar Sin ta hanyar fakewa da kalmar dimokaradiyya, yayin da har kullum gwamnatin kasar Sin ke nanata cewa, kare rayukan al’umma, da bunkasa ci gaban su, su ne a sahun gaba, idan ana maganar kare ’yancin al’umma, da mulkin dimokaradiyya na gaskiya.
Karkashin wannan mahanga, kasar Sin ta yi namijin kokarin kawar da talauci sama da abun da ake gani a daukacin kasashen yamma. Kaza lika ta yi nasarar dakile yaduwar cutar COVID-19 cikin gaggawa bisa matakai da suka baiwa duniya mamaki, yayin da dubun dubatar al’ummu a Amurka ke rasa rayukansu, sakamakon gazawar salon dimokaradiyya da Amurkar ke tutiya da shi.
Don haka dai, babban abun tambaya a nan shi ne, wace kasa ce ke nan za a ce ta gaza wajen kare ’yancin bil adama? Bahaushe dai kan ce “Ido ba mudu ba ne amma ya san kima”. (Saminu Alhassan)