logo

HAUSA

Firaministan Sudan ya umarci a saki mutanen da ake tsare da su

2021-11-25 11:05:30 CRI

Firaministan Sudan ya umarci a saki mutanen da ake tsare da su_fororder_211125-ahmad-3-Sudan

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok, a jiya Laraba ya baiwa jami’an tsaron kasar umarnin dakile zanga zangar da aka tsara a yau Alhamis tare kuma da gaggauta tsara hanyoyin sakin mutanen da ake tsare da su, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin firaminstan ta bayyana.

Hamdok, wanda ya ba da umarnin a yayin wani taron ganawa da shugabannin ’yan sandan kasar Sudan, inda suka yi nazari kan cikakken tsarin daidaita zanga-zangar kasar da kuma bayyana yadda al’umma za su iya gabatar da korafinsu ta hanyar lumana a matsayin wani hakkin da dokar kasa ta ba su, dokokin juyin juya halin Sudan sun yi sanadiyyar kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a shekarar 2019.

A cewar sanarwar, matakan sakin mutanen da ake tsare da su ya shafi dukkan kasar baki daya.

Mai yiwuwa ne babban birnin Khartoum, da sauran biranen kasar ta Sudan su sake fuskantar zanga zangar neman sakin fararen hula a yau Alhamis. (Ahmad Fagam)