logo

HAUSA

MDD: Gwamnatin Habasha ta ba da damar shigar da kayan tallafi zuwa yankin Tigray

2021-11-25 11:00:56 CRI

MDD: Gwamnatin Habasha ta ba da damar shigar da kayan tallafi zuwa yankin Tigray_fororder_211125-ahmad-1-Habasha

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD, ta ce kimanin manyan motoci 40 dauke da kayayyakin tallafin jin kai, da suka hada da kayan abinci, aka ba su damar shiga yankin Tigray mai fama da rikici na kasar Habasha a karon farko cikin sama da wata guda.

A cewar hukumar agajin ta MDD OCHA, manyan motocin sun tashi daga garin Semera dake shiyyar Afar zuwa yankin Tigray a ranar Talata. Wannan shi ne ayarin motoci na farko da aka samu tun a ranar 18 ga watan Oktoba.

Wasu motocin dauke da man fetur da magunguna har yanzu suna garin Semera inda suke jiran a tantance su.

OCHA ta kara da cewa, a halin yanzu akwai jiragen saman ayyukan jin kai da suka nufi Mekelle, babban birnin yankin Tigray, bayan dawowarsu bakin aiki a ranar Laraba bayan da aka dakatar da su a ranar 22 ga watan Oktoba. A sakamakon hakan, MDD da abokan huldar hukumar ba da agajin MDDr sun samu damar gudanar da kai kawon ma’aikatansu a yankin Tigray da kuma takaita adadin ayyukan dake shafar kudade a yankin.

To sai dai kuma, abokan huldar hukumar ba da agajin dake yankin a halin yanzu, suna ci gaba da fuskantar kalubaloli sakamakaon karancin kudade da suke fama da shi. (Ahmad Fagam)