Ya dace Amurka ta bi hanyar da ta dace don inganta alaka da Sin
2021-11-24 15:42:13 CRI
A makon da ya gabata ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tattauna da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta kafar bidiyo, inda shugaba Xi ya gabatar da wasu ka'idoji guda uku da za su daidaita alakar Sin da Amurka: Na farko, mutunta juna. Na biyu shi ne zaman tare cikin lumana. Kana na uku, hadin gwiwar samun nasara tare.
Xi Jinping ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su mai da hankali kan wasu muhimman abubuwa guda hudu a halin yanzu: Na farko, nuna nauyin da ke wuyansu a matsayinsu na manyan kasashen duniya, da jagorantar al'ummomin duniya wajen yin hadin gwiwa don tunkarar manyan kalubale. Na biyu shi ne inganta mu’amala a kowane mataki da kuma sassa daban-daban bisa tsarin daidaito da samun moriyar juna.
Na uku shi ne daidaita bambance-bambance da batutuwa masu muhimmanci ta hanya mai ma'ana, don ganin dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ba ta tabarbare ko shiga wani yanayi ba. Na hudu shi ne karfafa hadin kai da hadin gwiwa kan manyan batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyya-shiyya, don tabbatar da daidaito da adalcin tsarin kasa da kasa.
Wannan dai ita ce ganawar bidiyo ta farko da shugabannin biyu suka gudanar, tun bayan zantawa ta wayar tarho sau biyu da shugabannin kasashen biyu suka yi a wannan shekara, inda suka yi magana kan dabaru, da muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban dangantakar Sin da Amurka, da kuma muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Sun kuma amince cewa, ganawar ta kasance bisa gaskiya, mai inganci, ta kuma samar da sakamako mai kyau, wadda za ta taimaka wajen kara fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu, da kuma aikewa da sako mai karfi ga kasashen Sin da Amurka da ma duniya baki daya. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)