logo

HAUSA

Yan sandan Zamfara sun kubutar da mutane 24 da aka yi garkuwa da su

2021-11-24 10:03:06 CRI

Yan sandan Zamfara sun kubutar da mutane 24 da aka yi garkuwa da su_fororder_1124-Najeriya-Ahmad

Hukumar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da kubutar da mutane 24 daga hannun masu garkuwa, da suka hada har da wasu dalibai biyar, mutanen sun samu ’yancinsu ne yayin ayyukan sintiri da jami’an tsaron kasar suka gudanar a jihar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Ayuba Elkanah, kakakin hukumar ’yan sandan jihar Zamfara, ya bayyanawa taron manema labarai a Gusau, babban birnin jihar cewa, sun damka dukkan mutanen da aka kubutar ga gwamnatin jihar a ranar Talata.

A cewar Elkanah, daliban biyar sun shafe kusan watanni biyu a hannun masu garkuwar bayan da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi awon gaba da su a makarantu biyu na jihar dake kananan hukumomin Shinkafi da Kaura Namoda a watan Satumba.

Ya ce da yammacin ranar Litinin, jami’an tsaron suka ceto mutanen ta hanyar amfani da wasu bayanan sirri wajen kubutar da daliban biyar tare da wasu mutane takwas wadanda ’yan bindigar suka sace daga karamar hukumar Shinkafi.

Sannan kuma a ranar Litinin din, wata tawagar musamman ta kwararrun ’yan sanda da aka tura kan haryar Gusau-Tsafe-Funtua dake jihar, sun kubutar da wasu fasinjoji 11 wadanda ’yan fashin daji suka yi garkuwa da su a baya bayan nan. (Ahmad)