logo

HAUSA

Huawei ya horar da daliban Malawi 50 masu nazarin fasahar sadarwa

2021-11-24 10:16:05 CRI

Huawei ya horar da daliban Malawi 50 masu nazarin fasahar sadarwa_fororder_1124-Huawei-Malawi-Ibrahim

Kamfanin Huawei na kasar Sin ya horar da dalibai 50 'yan Malawi daga jami'o'i da kwalejojin kasar, karkashin shirin kamfanin mai suna “Seeds for the Future”.

Horon wanda aka yi wa lakabi da “2021 Industrial Digital Transformation Conference”, an fara shi ne tun a ranar 15 ga watan Nuwamba aka kuma kammala shi jiya Talata a Lilongwe, babban birnin kasar tare da ba da takardun shaida ga matasan da a yanzu suka sami sabon ilmi a fannin fasahar sadarwa (ICT).

Wakiliyar kamfanin Huawei dake kasar Angela Chuma, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kamar irin wannan horon da aka yi a baya a karkashin shirin, shirin samun horon na bana, ya bai wa daliban damar more fasahar sadarwar zamani, ta hanyar yin mu'amala da kwararrun kamfanin a fannin fasahar sadarwa da dai sauransu.

Chuma ta ce, shirin horon ya samu nasara sosai, kuma matasanmu masu basira, sun ga irin abubuwan da duniyar fasahar sadarwar zamani ke ciki, da kuma sabbin abubuwa dake tafe. Ta kara da cewa, daliban sun kuma samu damar yin mu'amala da kwararrunmu na kasar Sin ta hanyar tambayoyi da ba da amsoshi. Haka kuma daliban sun tattauna kai tsaye da dalibai daga wasu kasashe. (Ibrahim)