logo

HAUSA

Karon farko an bude sashen koyar da Sinanci a jami’ar Dakar dake kasar Senegal

2021-11-24 10:58:52 CRI

Karon farko an bude sashen koyar da Sinanci a jami’ar Dakar dake kasar Senegal_fororder_1

Jiya Talata, jami’ar Dakar dake kasar Senegal ta yi taron manema labarai inda ta bayyana cewa, ta bude sashen koyar da Sinanci a karon farko a jami’ar, abin da ya alamanta cewa, koyon Sinanci ya shiga tsarin ba da ilmi na kasar.

An ce, tun a shekarar 2012 lokacin da jami’ar Liaoning ta kasar Sin da jami’ar Dakar suka yi hadin gwiwa inda suka kafa kwalejin Confucius, Sin ta yi kokarin yin shawarwari da Senegal don shigar da fannin koyon Sinanci cikin tsarin ba da ilminta. Wannan fanni ya taimakawa kwalejin Confucius wajen samarwa dalibai takardar shaidar karatu a wannan bangare, abin da ya kara jawo hankalin dalibai dake sha’awar koyon Sinanci, kuma zai taimakawa kasashen biyu ta fuskar kara mu’ammala da tuntubar juna tsakaninsu.

Kwalejin Confucius zata hada kai da kwalejin koyon harsuna na jami’ar Dakar don ba da taimako wajen samar da littattafai da darasunan Sinanci da dai sauransu. (Amina Xu)