logo

HAUSA

Mashirya gasar Olympics ta birnin Beijing na maraba da zuwan kafafen watsa shirye shirya

2021-11-24 15:24:18 CRI

Mashirya gasar Olympics ta birnin Beijing na maraba da zuwan kafafen watsa shirye shirya_fororder_src=http___sports.workercn.cn_html_files_2021-11_18_20211118154916700581522&refer=http___sports.workercn

Kwamitin tsare tsare na shirya gasar Olympic da gasar nakasassu ta lokacin hunturu da za ta gudana a birnin Beijing a farkon shekarar dake tafe ko (BOCOG), sun yi maraba da daukacin sassan kafafen watsa shirye shirye da za su halarci gasar, wadda a cewar su za ta zamo a bude ga dukkanin sassa.

Kakakin kwamitin ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a karshen makon jiya. Ga kuma tambayoyin da ya amsa game da wannan batu.

Q: Wata kungiya mai suna "Kungiyar ‘yan jaridun kasashen waje ta Sin" a baya bayan nan ta nuna damuwa game da damar gabatar da rahotanni a yayin gasar ta birnin Beijing ta 2022. Ko BOCOG na da ta cewa game da hakan?

A: Da farko dai, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya bayyana, Sin ba ta san wannan kungiya ba. Don haka ba za ta wakilci ainihin muryar ‘yan jaridun kasashen ketare dake kasar Sin ba.

Gasar Olympic ta birnin Beijing ta 2022 babbar gasa ce mafi kasaita da za ta gudana a lokacin hunturu. Domin bude kofa ga kowa, BOCOG har kullum na maraba da zuwan dukkanin kafafen watsa shirye shirye na kasa da kasa, tun ma farko shirye shiryen gasar. Domin baiwa kafafen damar gudanar da ayyukan su, BOCOG ya gayyaci ‘yan jaridu daga ofisoshin su na birnin Beijing, don halartar ganawar bai daya, da sauran tattaunawa, da tarukan karawa juna sani, sun kuma ganewa idanun su shirin da ake yi a Beijing" da ayyukan gwajin gasar, an kuma gabatar da takardun bayanai da sauran su, domin sanar da kafofin watsa shirye shirye daga kasashe da yankuna na sassan duniya daban daban, game da halin da ake ciki don gane da shirya gasar.

Cikin watanni 12 da suka gabata, wasu ‘yan jaridu sun shiga an dama da su cikin ayyuka da dama, sun kuma karbi takardun bayanai har 28. Kari kan hakan, BOCOG ya shirya taron ganawa da manema labarai domin ‘yan jaridun dake kasar Sin a watan Janairu, da Fabarairu da Yuli na shekarar 2020, a sassa 3 na gudanar da gasar a Beijing, da Zhangjiakou da Yanqing.

Ga misali, yayin ziyara a Zhangjiakou, BOCOG ya gayyaci ‘yan jaridu daga kafofi 18, zuwa ziyarar yini 2 a sassan gudanar da gasar, kafofin sun hada da Associated Press, da Reuters, da Agence France-Presse, da Getty Images, da European Pressphoto Agency, da National Broadcasting Company. Sai kuma Kyodo News, da Tokyo Shimbun, da Agenzia Nazionale Stampa Associata, da Korean Broadcasting System, da Deutsche Presse-Agentur, da Sveriges Television, da Radio France Internationale. Sauran su ne Financial Times, da Russian News Agency TASS, da Russia Today, da kafar Talabijin ta Kazakhstan 24kz, da Kazinform.

Wuraren da ‘yan jaridun suka halarta sun hada da Genting Snow Park, da Guyangshu mai kunshe da kayayyakin gudanar da gasar daban daban, inda a lokacin jami’an gasar ta Beijing 2022, da masu lura da wuraren wasannin, da wadanda suka tsara wuraren suka bayar da cikakkiyar gabatarwa ga manema labaran da suka hallara.

Bugu da kari, BOCOG ya taimakawa kafofin watsa labarai 15, wajen samun iznin yayata gasar ta Beijing 2022. Ta hanyar wadannan damammaki na zantawa da su, ‘yan jaridun waje, sun samu cikakkun bayanai na ci gaban da ake samu game da shirya gasar, da fasahohin da aka tanada, da sabbin dabaru na wanzar da gasar, da ma yadda wasannin za su kara raya yankunan da za a gudanar da ita a cikin su.

Mun nanata cewa, domin kare dokoki, da ka’idojin dakile yaduwar COVID-19 na Sin, dukkanin ‘yan jaridun waje za su iya watsa shirye shirye game da gasar mai zuwa a cikin kasar Sin. BOCOG zai tabbatar da ‘yancin ‘yan jaridu game da watsa shirye shirya, daidai da tanajin yarjeniyoyin aikin su a biranen gasar da ka’idojin kasar. Kana za su samu damar yin aiki mai nagarta a Sin, kamar yadda aka saba tun a baya.

Q: Yaya BOCOG ya tsara aiwatar da matakan bunkasa watsa shirye shirye, da bukatar gudanar da zantawa da mutane?

A: BOCOG ya shirya gudanar da tattaunawa da ‘yan jarida cikin kwanaki masu zuwa. Tattaunawar da za ta samu halartar manyan masu ba da shawara, da sassan masu ruwa da tsaki dake lura da sashen ba da hidima, da ayyukan kafafen watsa labarai. Za su gana kai tsaye da ‘yan jaridu na kafofin waje dake bukatar zantawa da mutane.

Bisa yanayin COVID-19, da tsarin ayyukan da za su gudana a wuraren wasannin, za a gudanar da zantawa ta rukuni rukuni guda 3, ga ‘yan jaridu a ofishin birnin Beijing domin kafofin kasashen waje. Wuraren da za a ziyarta sun hada da babban filin zamiyar kankara na Oval, da kauyen wasannin Olympic na lokacin hunturu, da cibiyar wasanni dake Wukesong, da babbar cibiyar tsare tsare.

Yayin da ake ci gaba da gwaje gwaje, BOCOG zai kara adadin ‘yan jaridu da za su samu damar yayata wasannin gasar tsakanin kafafen kasashen waje. Kaza lika za a gudanar da taron ‘yan jaridu guda biyu nan da karshen shekarar nan, wadanda za a baiwa ‘yan jarida na gida da waje damar halarta.

Ko shakka ba bu, mun san cewa akwai bukatar karin masu son gabatar da rahotanni game da gasar yayin da lokaci ke kara karatowa. Adadin masu son zantawa da mutane da masu neman karin bayani na karuwa sosai a watanni 6 na biyun wannan shekara, inda daga watan Yuli kawo yanzu, muka samu adadin da ya kai 209. Domin biyan wadannan bukatu, BOCOG ya kebe jami’ai musamman domin lura da hakan, inda suke duba sakwannin email duk bayan sa’oi 2, tare da ba da amsa a kan lokaci. Jami’an za su tsara gudanar da tattaunawa, ko karbar bayanai daga sakwannin email da ake aikowa.

Kwamitin tsare tsaren gasar na ci gaba da bin manufar ba da amsa da yin bayani ga kowa, yana iya kokarin shawo kan kalubale da annobar COVID-19 ke haifarwa duniya, tare da taimakawa ‘yan jarida cimma burin su na gudanar da tattaunawa da mutane, a yayin gasar ba tare da wani bata lokaci ba.

Q: Ta yaya BOCOG zai tabbatar da an gabatar da rahotanni yadda ya dace a yayin gasar?

A: BOCOG na maraba da daukacin kafofin watsa shirye shirye daga dukkannin sassan duniya zuwa kasar Sin, domin su yayata gasar Olympic da ajin nakasassu na gasar ta Beijing ta 2022. Ya zuwa yanzu, sama da ‘yan jaridu masu aiki a kafofin dake rubuta labarai, da masu daukar hotuna 2,500 ne suka gabatar da bukatar su ta aiki a yayin gasar. A hannu guda kuma, BOCOG zai bude wuri na musamman a cibiyar watsa shirye shirye ta gasar, domin samar da hidimonin watsa shirye shirye da tsara bukatun masu shirya zantawa da mutane, da ma gabatar da tarukan ‘yan jarida na rana rana, tare da wakilan kwamitin shirya gasar, da nufin samar da isassun bayani ga ‘yan jaridu.

A lokaci guda kuma, BOCOG zai samar da wuraren cin abinci, da masaukai da hidimar sufuri a cikin yanayi mai kyau, ta yadda ‘yan jarida za su samu nishadin aiki a yayin gasar. Har ila yau, za a gudanar da tattaunawa ta yanar gizo, domin kara fadada yawan damar ‘yan jarida ta zantawa da masu ruwa da tsaki gwargwadon iko.

Bugu da kari, BOCOG na maraba da rahotanni gama da sassan gasar ta Beijing ta 2022, musamman bangaren shirye shirye, ciki har da wuraren da aka gina domin gasar, da tsarin gudanar da ita, yana kuma da burin karbar bukatar ziyarar gani da ido daga kafafen watsa shirye shirye, wanda hakan zai taimakawa kwamitin shirya gasar da dama kara inganta ayyukan sa.

Bari mu dage da aiki tukuru, mu mayar da hankali ga wasanni, da wannan gasa ita kan ta, mu samar da yanayi mai kyau, da labarai masu ban sha’awa daga masu halartar gasar, kana mu samar da yanayi mai dadi da zai ba da damar gudanar da gasar Olympic, da ajin gasar ta nakasassu ta lokacin hunturu dake tafe a nan kasar Sin.