logo

HAUSA

Karuwar farashin talotalo ya zama gargadi ga gwamnatin Amurka

2021-11-24 20:53:08 CRI

Karuwar farashin talotalo ya zama gargadi ga gwamnatin Amurka_fororder_hoto

Ranar Alhamis ta makon nan ce ranar bikin godiya na kasar Amurka, kuma ganawar iyalai tare da cin gasasshen talotalo su ne muhimman abubuwan da Amurkawa kan yi a wannan rana. Amma, bana, Amurkawa za su ci abincin dare mafi tsada a tarihi.

Bisa bayanin da ma’aikatar harkokin gona ta kasar Amurka ta fidda, farashin talotalo ya karu da kashi 21 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar bara. Kuma, bisa kididdigar da kungiyar hadin gwiwar gandun noma ta fitar, yawan kudin da Amurkawa za su kashe kan abincin bikin ranar godiya a bana, ya zama mafi tsada cikin shekaru 36 da suka gabata.

Karuwar farashin abincin bikin ranar godiya ya nuna karuwar farashin kayayyaki a kasar Amurka. Yanzu haka farashin abinci, da farashin makamashi, da farashin motoci da sauransu, dukkansu sun karu matuka a kasar. An fidda bayanin cewa, hauhawar farashi a watan Oktoba a kasar Amurka, ta riga ta kai matsayin koli cikin shekaru 31 da suka gabata.

Kafin haka kuma, gwamnatin kasar Amurka ta fidda shirin raya tattalin arziki mai kunshe da dallar Amurka sama da triliyan daya, amma kuma gazawar kasar a fannin yaki da cutar COVID-19, ya sa ba ta samu farfadowar kasuwanni kamar yadda ta yi fata ba.

Ban da haka kuma, ci gaba da manufarta ta kara karbar haraji daga kasar Sin, ya haddasa karuwar fasahin kayayyaki cikin kasar.

A halin yanzu, ba kawai matsalar hauhawar farashi ce ke matsawa al’ummun Amurka lamba ba, har ma matsalar za ta haddasa illa ga al’ummomin sauran kasashen duniya. Ya kamata kasar Amurka ta dauki matakan kudade masu dacewa, da kuma yin hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa wajen daidaita matakan kiwon lafiya, domin inganta farfadowar kasuwannin kasashen duniya. (Maryam)