logo

HAUSA

Kasar Sin Daya Ce Tak A Duniya

2021-11-24 19:14:01 cri

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce kadai halastacciyar gwamnati dake wakiltar kasar Sin. Haka kuma wanzuwar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce babbar manufar da kasashen duniya suka amince da ita, kana tushen siyasa na raya hulda tsakanin Sin da duk kasashen da suka kulla ko ma suke fatan kulla alaka da kasar Sin.

Yanzu haka akwai kasashe 180 a duniya, wadanda suka amince tare da goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma wannan ita ce yarjejeniya ta gaskiya da kasashen duniya suka amince da ita.

Amma duk da wannan manufa, har yanzu ana samun wasu makiya kasar Sin da ma wasu kasashe ko dai cikin rashin sani ko neman takalar fada, suke kokarin keta wannan manufa. Koda a kwanakin baya ma, kasar Lithuania ta yi biris tare da lalata tushen siyasa na huldar jakadanci dake tsakaninta da kasar Sin, yayin da ta amincewa yankin Taiwan ya bude ofishin wakilci a kasarta, wannan ya sa kasar Sin ta yanke shawarar rage matsayin huldarsu domin kiyaye cikakken ikon mallakar kasarta.

Taiwan dai ba kasa ba ce, wani bangare ne na kasar Sin. Duk abun da ’yan aware suke yi na jirkita gaskiya, sam ba zai taba canja gaskiyar lamarin ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan duka suna karkashin ikon Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin.

A kokarin da kasar Sin ke yi na kara fahimtar da kasashen duniya game manufar kasar Sin daya tak a duniya, sanarwar da aka fitar bayan kammala cikakken zaman karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, a kwanakin nan, ta bayyana karara cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma matsaya irin wannan da aka cimma a shekarar 1992, wadda ke adawa da ayyukan ’yan aware dake neman ’yancin kai na Taiwan, da tsoma baki daga waje. Wannan ya nuna a fili irin tsayin daka na kasar Sin, da kuma matsayinta na kare ikon mallakar kasa, da tsaro da moriyar ci gabanta.

Kuma duk kasar dake son ta kulla huldar diflomasiya da kasar Sin, waijibi ne ta martaba wannan manufa. Wato kasar Sin daya ce tak a duniya. Don haka, Ba A Sauyawa Tuwo Suna.