logo

HAUSA

An fara watsa shirin “Dandanon Macao” don taya murnar cika shekaru 22 da dawowar yankin Macao kasar Sin

2021-11-24 21:37:36 CRI

An fara watsa shirin “Dandanon Macao” don taya murnar cika shekaru 22 da dawowar yankin Macao kasar Sin_fororder_211124-Macao-Maryam-hoto

Yau Laraba, an yi bikin fara watsa shirin “Dandanon Macao” a birnin Guangzhou na kasar Sin, domin taya murnar cika shekaru 22 da dawowar yankin Macao kasar Sin. Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da yankin musamman na Macao ne suka tsara shirin cikin hadin gwiwa.

Shugaban yankin Macao Ho Iat Seng, da mataimakin ministan harkokin fadakar da jama’a na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana, shugaban CMG Shen Haixiong sun halarci bikin. (Maryam)