logo

HAUSA

Kitsa makarkashiya don bata alakar Sin da Afirka da Amurka ta yi ba zai ci nasara ba

2021-11-23 21:46:48 CRI

Kitsa makarkashiya don bata alakar Sin da Afirka da Amurka ta yi ba zai ci nasara ba_fororder_A

Kwanan nan ne sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya ziyarci kasashen Kenya da Najeriya da kuma Senegal. Ga alama wannan karon, Blinken bai tilastawa kasashen Afirka su zabi wata kasa ba, amma hakikanin gaskiya, ya yi yunkurin kitsa makarkashiya don bata alakar Sin da Afirka, da kawo tsaiko ga harkokin diflomasiyyar kasar Sin.

Amma babu yiwuwar a bata dangantakar abuta da hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kuma akwai kwararan shaidu. A nasa bangaren, ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya Geoffrey Onyeama ya mayar da martani ga kalaman Blinken, inda ya ce, abun da muke lura a nan shi ne babban zarafin da muke samu wajen hada kai tare da mutanen kasar Sin. Suna da kwarewa sosai a fannin manyan gine-gine da sauran muhimman more rayuwar al’umma.

Sahihanci tsakanin aminai ya fi muhimmanci. Amurka ba ta taba lura da samar da ci gaba ga nahiyar Afirka ba, amma tana amfani da Afirka don neman cimma muradun siyasa.

Kitsa makarkashiya don bata alakar Sin da Afirka da Amurka ta yi ba zai ci nasara ba_fororder_B

Amma ita kasar Sin ta kan cika alkawarin da ta daukawa kasashen Afirka. Kwanan nan ne wani gidan talabijin na kasar Zimbabwe ya wallafa wani shiri, inda ya bayyana yadda alluran riga-kafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar suka taimaka sosai wajen yaki da cutar, da farfado da sana’ar yawon shakatawa gami da tattalin arziki a wurin. Rahotannin sun kuma ce, sama da kaso 95 bisa dari na alluran riga-kafin cutar da aka yiwa al’ummar Zimbabwe, na kasar Sin ne.

Ya dace Amurka ta saurari ra’ayin wani kwararre daga kasar Afirka ta Kudu mai suna Eric Olander, inda ya ce, gwamnatin Amurka ba za ta ci nasara ba idan ta ci gaba da nuna ja-in-ja da kasar Sin. Ya kamata manyan jami’an Amurkar su karkata hankalinsu daga rawar da kasar Sin ke takawa a Afirka, zuwa yadda za su dauki matakan zahiri don samar da ci gaban nahiyar. (Murtala Zhang)