Sirrin kasar Sin na raya tattalin arzikinta cikin sauri
2021-11-23 20:05:41 CMG
Wasu abokaina ‘yan Najeriya su kan tambaye ni: “Ta yaya kasar Sin ta samu damar raya tattalin arzikinta cikin matukar sauri?” Suna kallon tasowar kasar Sin tamkar wani abun al’ajabi, inda ta dade tana samun karuwar tattalin arziki da ta kai kimanin kashi 10% a kowace shekara, kana jimillar GDPn kasar kan mutum guda ya tashi daga dalar Amurka 194 ta shekarar 1980, zuwa dala 10,503 ta shekarar 2020, ta yadda kasar ta canza matsayinta daga kasa mai fama da koma bayan tattalin arziki zuwa kasa mai matsakaiciyar wadata. Ban da wannan kuma, kasar ta cimma burinta na fitar da dukkan mutanen kasar masu karamin karfi daga kangin talauci. Sai dai mene ne “Sirrin” kasar Sin a fannin raya tattalin arziki?
A kwanan baya, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake rike da ragamar mulkin kasar ta kira wani taro, inda ta takaita wasu nasarori da fasahohin da aka samu a kasar cikin tarihin jam’iyyar na shekaru 100, ciki har da fasahohin kasar Sin a fannin raya tattalin arzikin kasa, wadanda suka shafi fannoni guda 8:
Na farko, shi ne neman ci gaban kasa ba tare da tsayawa ba. Saboda jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana kallon kare moriyar jama’a wani babban aiki nata, don haka tana ta kokarin raya tattallin arziki, gami da kyautata zaman rayuwar jama’a.
Na biyu, zurfafa gyare-gyaren da ake yi a kasar. Kasar Sin na ta kokarin daidaita manufofinta, don neman biyan bukatun raya tattalin arziki, da ma harkokin al’adu.
Na uku, a tsaya kan bude kofar kasar ga sauran kasashe. Kasar Sin tana kokarin samar da damammakin mu’amala da sauran kasashe, gami da hadin gwiwa tare da su.
Na hudu, shi ne dora matukar muhimmanci kan kirkiro sabbin fasahohi. Kasar Sin na yin amfani da sabbin fasahohi na zamani, gami da ingantattun manufofi, don sa kaimi ga ci gaban masana’antu.
Na biyar, kasar Sin tana kula da dukkan kamfanonin mallakar gwamnati, da kamfanoni masu zaman kasu, inda take samar musu da daidaiton damammakin samun ci gaba.
Na shida, shi ne kasar ta ba kasuwanni damar daidaita harkokin ciniki, gami da samar da nagartattun manufofi, don baiwa kamfanoni wani muhalli mai kyau.
Na bakwai, shi ne yadda kasar take magance daukar matakai marasa dacewa. Da farko ta tabbatar da zaman karko a fannin ci gaban tattalin arzikinta, sa’an nan ta nema a raya shi cikin sauri.
Na takwas, shi ne a tabbatar da matsayi na jagora na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Ta haka, aka tabbatar da dorewar manufofin kasar, da wani yanayi na zaman karko na tattalin arzikinta.
Hausawa su kan ce, “Tafiya maganin gari mai nisa”. Tabbas, abun da ya faru a kasar Sin a shekarun baya tamkar hakan ne, domin kuwa gwamnatin kasar ta sanya wani buri na raya tattalin arziki, daga baya a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar, daukacin al’ummun kasar sun hada karfi da karfe, wajen kokarin neman dabaru, da gyaran manufofi, don daidaita duk wata matsalar da suka gamu da ita, yayin da suke neman ciyar da tattalin arzikin kasar gaba. Bayan sun dade suna yin haka, rayuwar jama’ar kasar ta samu ingantuwa kwarai da gaske. (Bello Wang)