logo

HAUSA

Abokai su ne wadanda suke kokarin taimakawa juna

2021-11-23 11:09:10 CMG

Abokai su ne wadanda suke kokarin taimakawa juna_fororder_1

A jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron cika shekaru 30 da kulla huldar musayar ra’ayi tsakanin kasar Sin da kungiyar kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya ta ASEAN, inda ya sanar da kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin bangarorin 2.

Ban da wannan kuma, shugaban ya ba da shawarwari 5 dangane da yadda za a ci gaba da raya huldar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN a nan gaba, wadanda suka hada da kare zaman lafiya, da tabbatar da kwanciyar hankali, da ci gaban tattalin arziki, da kokarin kiyaye muhalli, da sada zumunta. Wadannan shawarwarin sun nuna matakan da za a dauka a kokarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kungiyar ASEAN, da yadda kasar Sin take nuna cikakken sahihanci a kokarin kulla hulda mai kyau tare da kasashe makwabtanta.

A cewar shugaba Xi, ya kamata kasashen kungiyar ASEAN da kasar Sin su zama tamkar ’yan uwa, inda suke kokarin taimakawa juna idan daya daga cikinsu ya gamu da matsala. Muddin aka dora cikakken muhimmanci kan burin jama’ar kasashe daban daban na kyautata zaman rayuwarsu, da kokarin inganta huldarsu da ta shafi manyan tsare-tsare, to, tabbas ne za a samu karin ci gaban tattalin arziki a kasashen kungiyar ASEAN gami da kasar Sin. (Bello Wang)

Bello