logo

HAUSA

Masana sun ce shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ ne hadin gwiwa mafi samun karbuwa a duniya

2021-11-22 20:33:41 cri

Masana sun ce shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ ne hadin gwiwa mafi samun karbuwa a duniya_fororder_src=http___pic.cyol.com_img_20211120_img_969f67fd5c076dc0415c7b7c9a5430edd6_c&refer=http___pic.cyol

A muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a wajen taron da ya gudana kwanan baya kan shawarar “ziri daya da hanya daya,” (BRI), ya zayyana alkiblar inganta hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, kamar yadda masana da shugabannin ’yan kasuwar kasa da kasa suka bayyana. Haka zalika, sun kuma amince da shawarar ‘BRI’ a matsayin hanyar bunkasa ci gaban duniya na bai daya, kana hanyar dake amfanawa al’ummun kasa da kasa. Farfesa Sheriff Ghali, shehun malami a tsangayar nazarin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja, a Najeriya, ya bayyana cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya,” ta kasance a matsayin wani dandalin hadin gwiwar kasa da kasa mafi samun karbuwa, kuma tana cigaba da taimakawa kasashen Afrika wajen inganta kayayyakin more rayuwa, da suka hada da fannin sufuri da lantarki da makamantansu. Diaa Helmy, sakatare janar ta majalisar bunkasa cinikayya ta Masar da Sin dake da ofishinta a birnin Alkahira, ta ce, shawarar ‘BRI’ ta kara tabbatar da samun nasarori da kuma bayar da gagarumar gudummawa a shekaru da dama da suka gabata wajen bunkasa ci gaba, da zamanintar da tattalin arziki, da bunkasa kayayyakin more rayuwa a kasashe da dama dake karkashin shawarar. Helmy ta ce, gudunmawar ‘BRI’ ta kara tabbatarwa a bayyane cewa, shawara ce da aka gina ta bisa hadin gwiwa, da cudanyar moriyar juna dake shafar dukkan bangarori. Yayin taro karo na 3 kan shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ da ya gabata a karshen mako a Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimman burikan ci gaba na shawarar. Yana mai cewa, amfanawa rayuwar jama’a, daya ne daga cikinsu. Shi ma wani masanin kasar Kenya ya bayyana cewa, hanyoyin bunkasa dangantakar Sin da Afrika, ta hanyar dandalin FOCAC da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ sun taimaka wajen samar da kyakkyawar makomar ci gaban nahiyar Afrika. Peter Kagwanja, wanda shi ne shugaban cibiyar nazarin manufofin Afrika ya ce, dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, tamkar wasu tagwayen injina ne na karfafa ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika. Ya ce shawarar BRI ta kasance tamkar wani asusun dake samar da kudaden aiwatar da muhimman ayyukan bunkasa cigaba da aka tsara. Masanin ya ce Afrika ta ci babbar moriya karkashin shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, ya ce shirin ya tallafawa ayyuka masu yawa na gina kayayyakin more rayuwa kamar gina hanyoyin mota, da layukan dogo, da tashoshin ruwa, tare da hade sassa da dama na kasashen Afrika. Cikin shekaru 8 da suka gabata, shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ ta samu tagomashi, inda ta yi fice a duniya. Ta kuma zama madubi ga kasar Sin wajen fadada bude kofarta da inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama. Wani rahoton nazari na bankin duniya, ya ce zuwa shekarar 2030, ana sa ran shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ za ta taimaka wajen fitar da mutane miliyan 7.6 daga matsanancin talauci, yayin da za ta fitar da wasu miliyan 32 daga matsakaicin talauci. (Ahmad Fagam)