logo

HAUSA

Gwamnatin Habasha da al’ummar kasar sun yi Allah wadai da kafafen yada labaran yamma saboda kirkirar labaran bogi

2021-11-22 14:16:50 CRI

Gwamnatin Habasha da al’ummar kasar sun yi Allah wadai da kafafen yada labaran yamma saboda kirkirar labaran bogi_fororder_1122-Habasha-Ahmad

A kwanan nan, hukumar kula da kafafen yada labaran kasar Habasha ta fitar da wasikun gargadi ga wasu manyan kafafen yada labarai na duniya hudu, da suka hada da CNN, BBC, Reuters, da kuma kamfanin yada labarai na AP, inda hukumar ta bayyana cewa, sun kirkira tare da yada labaran karya a yayin da suke gabatar da rahotanni game da batun dake shafar rikicin yankin Tigray na kasar Habashan. Rahoton da suka yada wanda ya haifar da kiyayya a tsakanin al’umma ya zubar da kimar ikon da gwamnatin Habashan ke da shi na tafiyar da yankunanta. Gwamnatin Habasha da al’ummar kasar sun bayyana adawarsu game da abubuwan da kafafen yada labaran yammacin duniya suke aikatawa. (Ahmad)