logo

HAUSA

Sharhi: Sai wanda ya sa takalma ya san ko sun dace

2021-11-22 20:20:20 CRI

 

Sharhi: Sai wanda ya sa takalma ya san ko sun dace_fororder_63d9f2d3572c11df4f28d163102716d9f603c2fb

Daga ranar 15 zuwa 20 ga wata, sakataren harkokin waje na Amurka Antony Blinken ya kai ziyara kasashen Kenya da Nijeriya da Senegal. A yayin ziyararsa a Nijeriya, bayan zantawa da shugaban kasar da ma mataimakinsa, ya kira taron manema labarai tare da takwaransa na Nijeriya Geoffrey Onyeama, kuma a yayin da yake amsa tambayar ‘yan jarida, ya ce yadda kasar Sin ke zuba jari tare da gine-gine a Afirka abu ne mai kyau, sai dai kuma ya zargi kasar Sin da haifar da matsalar basussuka ga kasashen Afirka.

Amma nan da nan furucinsa ya jawo suka daga wajen Mr. Geoffrey Onyeama, wanda ya ce, basussukan da Nijeriya ta ci ba su da yawa, wadanda Nijeriya ke iya biya ne, kuma dalilin da ya sa aka zabi kamfanonin kasar Sin wajen bunkasa manyan ababen more rayuwa a kasar shi ne, kamfanonin sun kware, kana suna samar da farashi mai rahusa. Ya jaddada cewa, “ciniki mafi kyau muke magana, a maimakon zancen wannan kasa ko waccan kasa.”

A hakika, Amurka ta saba da shafa wa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka kashin kaji bisa zargin wai “kasar Sin ta tsunduma kasashen Afirka cikin matsalar basussuka”.  Amma shin ko da gaske ne hakan abun yake? Alkaluman da muka samo daga shafin yanar gizo na ofishin kula da basussuka na Nijeriya(DMFN)sun yi nuni da cewa, ya zuwa watan Oktoban shekarar 2021, yawan basussukan da Nijeriya ta ci daga kasar Sin bai wuce kaso 3.94% kacal cikin jimillar basussukan da kasar ta ci, a yayin da hukumomin kudi da ma sauran sassa suke rike da kaso 3/4 na basussukan. A yayin da kasar Sin take hadin gwiwa da kasashen Afirka, ba ta taba tsoma baki cikin harkokin gidansu ba, haka kuma ba ta taba gindaya sharuddan siyasa ba.

Sharhi: Sai wanda ya sa takalma ya san ko sun dace_fororder_dbb44aed2e738bd4d1cd496996af2dde267ff9a3

Sinawa kan ce, sai wanda ya sa takalma ya san ko sun dace. Jama’ar Nijeriya da na Afirka ne suka dace su yi magana a kan ko hadin gwiwarsu da kasar Sin ya amfane su ko a’a. Kullum kasar Sin tana bin manufar mutunta juna, da cimma moriyar juna, a yayin da take hadin gwiwa da hulda da kasashen Afirka, musamman ma bisa ga dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, da ma shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka na kara ingantawa, tare da samar da gaggaruman nasarori. In mun dauki misali da Nijeriya, da layin dogon da ya hada Abuja da Kaduna, da layin dogo na Lagos-Ibadan, da ma tashar filin jirgin sama ta Abuja, da kuma tashar jiragen ruwa ta Lekki…… jerin ayyukan more rayuwa ne da aka gina a kasar, wadanda suka warware matsalolin da ke yi wa ci gaban tattalin arzikin kasar tarnaki, tare da kyautata rayuwar al’ummar kasar, wadanda suka samu karbuwa da amincewa daga gwamnatin kasar da ma al’ummarta.

Idan Amurka ta iya samar da hadin gwiwar da ke biyan bukatun Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka, lallai, za ta samu karbuwa a wurinsu. Kamar dai yadda minista Geoffrey Onyeama ya ce, “Nijeriya ta kiyaye hulda mai kyau da kasashen Sin da Amurka, kuma za ta daidaita huldarta da kasashen biyu bisa moriyarta, a maimakon moriyar Amurka ko ta kasar Sin.” A hakika, Nijeriya ta san ta yaya za ta fi amfana da hadin gwiwar da take yi da kasa da kasa, kuma ba ta bukatar “mai basira” ya fadakar da ita.

Sharhi: Sai wanda ya sa takalma ya san ko sun dace_fororder_186

Nan da wasu kwanaki masu zuwa, za a kira taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka(FOCAC). A gun taron manema labarai da aka kira a kwanan baya, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Qian Keming ya bayyana cewa, alkaluma sun yi nuni da cewa, daga watan Janairu zuwa na Satumban wannan shekara, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka ya bunkasa daga dukkan fannoni. Daga cikin alkaluman, kudin ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 185.2, adadin da ya karu da kaso 38.2%, wanda har ya kai matsayin koli a tarihi. Ministan ya ce, “nasarorin sun shaida hadin kan sassan biyu da ma kokarin da suka yi.”

Taron FOCAC da za a kira, tabbas zai kara inganta daidaito a tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda kuma zai nuna alkiblar samun dauwamammen hadin gwiwa mai inganci a tsakaninsu.

Sai dai kuma, muna fatan Mr. Antony Blinken zai mai da hankali a kan aiwatar da ayyukan da za su amfani kasashen Afirka, a maimakon bata huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka. Muna kuma fatan ganin Amurka din ta zama aminiyar da za ta samar da taimakonta ga ci gaban kasashen Afirka. (Lubabatu Lei)