logo

HAUSA

Gidauniyar saukaka fatara ta Sin ta gina tashoshin samar da ruwa mai tsafta a makarantun Habasha

2021-11-21 16:37:26 CRI

Gidauniyar saukaka fatara ta Sin ta gina tashoshin samar da ruwa mai tsafta a makarantun Habasha_fororder_211

Wata gudauniyar yaki da fatara ta kasar Sin (CFPA), da abokan huldarta sun damka tashoshin samar da ruwa mai tsafta da suka gina a makarantun gwamnati dake fadin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, a ranar Lahadi.

CFPA, tayi hadin gwiwa da kungiyar Splash International, wata kungiya ce mai zaman kanta, inda suka gina wuraren samar da ruwa mai tsafta, bayan samun tallafin kudi daga katafaren kamfanin gine-gine na Xuzhou na kasar Sin, (XCMG).

Abiy Tefera, daraktan shirin inganta makarantu na hukumar bunkasa ilmi ta birnin Addis Ababa, ya bayyana cewa, sabbin tashoshin samar da ruwa mai tsaftan da aka gina zasu amfanawa sama da yara ‘yan makaranta 23,000 a makarantu 20 dake babban birnin kasar ta Habasha.

Tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021, gidauniyar CFPA da hadin gwiwar Splash International, sun kafa manyan tsarukan tace ruwa guda 23, da na’urorin samar da ruwan sha mai tsafta 157, da kuma wuraren tsaftace hannu 152 a makarantu 20 dake birnin Addis Ababa.(Ahmad)