logo

HAUSA

Sakataren harkokin wajen Amurka ya ziyarci Nijeriya

2021-11-19 10:05:20 CRI

Sakataren harkokin wajen Amurka ya ziyarci Nijeriya_fororder_211119-Faeza 1-Blinken

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken dake ziyara a Nijeriya, ya isa birnin Abuja jiya Alhamis, inda ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari, tare da wasu jami’an gwamnati, game da bangarorin da gwamnatin Amurka ke da sha’awar hada gwiwa da kasar ta yammacin Afrika.

Wata sanarwa da fadar shugaban Nijeriya ta fitar, ta ce Shugaba Buhari da Antony Blinken, sun tattauna game da batutuwan da suka shafi tsaron yankin da sauyin yanayi. Sanarwar ta kuma ruwaito Blinken na cewa, Amurka da Nijeriya suna da kalubale mabanbanta, amma kuma muradinsu daya ne wato tsaro, yana mai fatan kyautata hadin gwiwa a tsakaninsu.

Yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da ministan harkokin wajen Nijeriya, Geoffrey Onyeama a Abuja, Antony Blinken ya bayyana tsaro da ilimi da kiwon lafiya da sauyin yanayi da muhimman ababen more rayuwa a matsayin bangarorin da kasarsa ke son zurfafa hadin gwiwa da Nijeriya, karkashen shirin raya kasashe na Amurka wato USAID.

Nijeriya ce kasa ta biyu cikin uku da Blinken zai ziyarta a rangadinsa a Afrika, inda ya fara tsayawa a Kenya a ranar Laraba, zai kuma kammala da Senegal a karshen makon nan. (Fa’iza Mustapha)