logo

HAUSA

Hidimar yanar gizo ta koma Sudan

2021-11-19 10:43:52 CRI

Hidimar yanar gizo ta koma Sudan_fororder_211119-Saminu 2-Sudan

Kamfanin dillancin labarai na SUNA ya rawaito cewa, a jiya Alhamis kafofin yanar gizo sun fara dawowa a sassan kasar Sudan, bayan toshe su da aka yi tun daga ranar 25 ga watan Oktoban da ya shude. Yanzu haka dai hidimar yanar gizo na dawowa sannu a hankali kan layuka daban daban da al’ummar Sudan din ke amfani da su.

Dakatar da kafofin yanar gizo a Sudan na cikin matakan da babban kwamandan dakarun sojin kasar Abdel Fattah Al-Burhan ya dauka, wadanda suka hada da rushe majalissar zartaswa da gwamnatin kasar.  (Saminu)