logo

HAUSA

Kamfanonin magani na Pfizer, Biontech da Moderna sun yi cinikin riga kafi na dala 1000 cikin sakon guda

2021-11-19 15:19:51 CRI

Kamfanonin magani na Pfizer, Biontech da Moderna sun yi cinikin riga kafi na dala 1000 cikin sakon guda_fororder_211119-ahmad 3-vaccine

Wata sabuwar kididdiga ta nuna cewa kamfanonin hada magunguna uku na Pfizer, Biontech da Moderna, sun samu ribar cinikin riga-kafin Covid-19 wacce ta kai kusan dala 65000 cikin kowane minti guda, sai dai kuma, galibin mutane dake kasashe matalauta har yanzu ba su samu riga kafin ba.

Kungiyar people's vaccine Alliance (PVA), wata kungiya mai zaman kanta wacce ta fidda wannan rahoto, ta fito karara ta bayyana cewa, kamfanonin uku sun sayar da mafi yawan alluran riga-kafinsu ne ga kasashe masu arziki, amma sun jefa kasashe masu karancin samun kudaden shiga cikin hadari. (Ahmad)