logo

HAUSA

Tilas ne Lithuania ta girbi mummunan sakamakon makircin ta

2021-11-19 16:09:57 CRI

Tilas ne Lithuania ta girbi mummunan sakamakon makircin ta_fororder_211119-(改编版)《国际锐评》:立陶宛必须承担背信弃义的一切后果

Duk da matukar adawa da Sin ta nuna, da kuma tattaunawa a lokuta mabanbanta, gwamnatin Lithuania ta yi gaban kan ta wajen amincewa da kafa ofishin da wai aka ce na wakilcin yankin Taiwan ne a kasar. Ko shakka babu, hakan keta hurumin manufar kasar Sin daya tak a duniya ne, kuma mataki ne na tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, da yin watsi da alkawarin siyasa dake cikin yarjejeniyar da kasashen biyu suka amince, mai nasaba da huldar diflomasiyyar su.

Hakika Sin za ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba, domin kare ikon mulkin kai, da tsaron yankunanta, kuma Lithuania za ta girbe mummunan sakamakon danyen aikin ta.

Ga kasar Sin, batun yankin Taiwan muhimmin lamari ne mai matsayin koli. Kuma wannan alaka da Lithuania take neman kullawa da Taiwan, za ta zame mata babbar matsala. Manufar kasar Sin daya tak a duniya ka’ida ce da sassan kasa da kasa suke amincewa, kuma manufar siyasa ce da Sin ke bi wajen bunkasa kawancen ta da sauran kasashen duniya.

Bugu da kari, Sin ta sha nanata aniyar gwamnati, da daukacin al’ummar Sinawa, ta cimma nasarar dunkulewar sassan ta, matakin da ya zama jigo ga burinta na kare ikon mulkin kai, da tsaron yankunan ta, wanda kuma ba za ta bari a keta hurumin sa ba. (Saminu Alhassan)