logo

HAUSA

Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren arewa maso yammacin Najeriya ya kai 43

2021-11-19 10:31:41 CRI

Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren arewa maso yammacin Najeriya ya kai 43_fororder_211119-ahmad 2-Sokoto

Yawan mutanen da suka mutu a hare-haren da ’yan bindiga suka kaddamar a farkon wannan mako a wasu kauyukan dake kananan hukumomi biyu na jihar Sokoto ya karu zuwa mutane 43, kamar yadda ofishin gwamnan jihar Sokoto dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriyar ya tabbatar da hakan.

A sanarwar da ofishin gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya fitar, ta ce, yawan mutanen da suka mutu a harin kananan hukumomin Illela da Goronyo ya karu daga mutane 15 zuwa 43, inda aka bayyana hakan yayin da gwamnan da sauran jami’an gwamnati suka ziyarci yankunan a ranar Laraba.

Hare haren an kaddamar da su ne a daren Lahadi har zuwa wayewar garin Litinin, kamar yadda gwamna Tambuwal ya tabbatar cikin wata sanarwar da ya fitar, ya ce ’yan bindiga wadanda aka fi sani da ’yan fashin daji ne suka kaddamar da munanan hare haren. (Ahmad Fagam)