logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi tir da kakaba takunkumi ko barazana da nufin tsoma bakin cikin harkokin gidan wasu kasashe

2021-11-19 10:08:13 CRI

Kasar Sin ta yi tir da kakaba takunkumi ko barazana da nufin tsoma bakin cikin harkokin gidan wasu kasashe_fororder_211119-Saminu 1-Zhao Lijian

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na Allah wadai da matakin Amurka na kakaba takunkumi, ko barazanar matsin lamba, da nufin samun damar tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne a jiya Alhamis, yayin da yake martani ga matakin Amurka na kakabawa Eritrea takunkumin tattalin arziki. Jami’in ya ce har kullum, Sin na fatan ganin sassan kasa da kasa sun rungumi musaya bisa dokokin kasa da kasa, da ka’idojin cudanyar kasashe daban daban.

Zhao ya ce "Bisa shaidu daga abubuwan da suka wakana a baya, takunkumai da wasu kasashe ke kakabawa wasu bisa radin kan su, ba sa haifar da zaman lafiya da lumana a yankunan da kasashen suke. Maimakon hakan ma, takunkuman na haifar da illa ne ga ci gaban tattalin arziki da walwalar al’ummun su, lamarin da ke matukar shan suka daga sassan kasa da kasa.

Don haka dai a cewar Zhao, Sin na fatan daukacin sassan kasa da kasa za su yi taka tsantsan game da irin matakan da suke aiwatarwa, su kuma taka rawar da ta dace, wajen wanzar da zaman lafiya da lumana a yankin kahon Afirka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, a ranar 12 ga watan Nuwambar nan, sashen baitulmalin Amurka, ya fitar da sanarwa dake tabbatar da kakaba takunkumi ga wasu sassa 4, da wasu mutane 2, ciki har da ma’aikatar tsaron Eritrea, da jami’iyyar PFDJ mai mulkin kasar, da kuma mashawarcin shugaban kasar kan harkokin tattalin arziki. Matakin dai ya samu sa hannun shugaban Amurka Joe Biden.   (Saminu)