logo

HAUSA

Xi Jinping ya jaddada manufar samar da matakai masu kyau don bunkasuwar shawarar ziri daya da hanya daya

2021-11-19 20:00:16 CRI

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron dandalin raya shawarar ziri daya da hanya karo na uku da aka gudanar a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, tare da gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya jaddada cewa, dole ne a sa kaimi ga samar da kyakkyawan matsayi, mai dorewa, da inganta rayuwar jama'a, da karfafa tushen hadin gwiwar dake tsakanin kasashe, da fadada sabbin fasahohi ga hadin gwiwar kasa da kasa, don habaka shawarar ziri daya da hanya daya mai inganci da ci gaba da samun sabbin sakamako.(Ibrahim)