logo

HAUSA

Xi zai halarci taron koli na murnar cika shekaru 30 da kafa kawancen Sin da ASEAN ta kafar bidiyo

2021-11-19 15:37:03 CRI

Xi zai halarci taron koli na murnar cika shekaru 30 da kafa kawancen Sin da ASEAN ta kafar bidiyo_fororder_211119-ahmad 4-Sin da Asean

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta tare da jagorantar taron kolin murnar cika shekaru 30 da kulla dangantaka tsakanin Sin da kungiyar kasashen gabashin Asiya wato (ASEAN), daga birnin Beijing a ranar 22 ga watan Nuwamba.

Taron kolin zai gudana ne ta kafar bidiyo, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar a yau Juma’a. (Ahmad)