logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijer ya zanta da firaministan Nijer game da alakar kasashen biyu

2021-11-19 10:23:41 CRI

A ranar 18 ga wata, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Nijer Jiang Feng ya tattauna da firaministan Nijer Ouhoumoudou Mahamadou, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan cigaban da aka samu game da huldar dake tsakanin Sin da Nijer.

Jakada Jiang Feng, ya isar da gaisuwar fatan alheri ta firaministan kasar Sin Li Keqiang, da kuma kyakkyawar fata ga firaminista Ouhoumoudou Mahamadou, inda ya bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, dangantakar dake tsakanin Sin da Nijer ta yi matukar bunkasa kuma tana ci gaba da kyautatuwa, dangantakar siyasa a tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da inganta, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen ta samar da kyawawan sakamako, kana alakar dake tsakanin mutum da mutum da cudanyar al’adu ta kara kusantar da juna a tsakanin bangarorin. A matsayinsa na sabon jakadan kasar Sin a Nijer, zai yi aiki tukuru tare da Nijer domin daga matsayin cikakkiyar dangantaka mai zurfi da hadin gwiwar aminantaka tsakanin Sin da Nijer.

Firaminista Ouhoumoudou Mahamadou ya yi maraba da jakada Jiang Feng, yayin da yake kama aiki, kana ya bukaci jakada Jiang ya isar da gasuwarsa tare da girmamawa ga firaminista Li Keqiang. Ouhoumoudou Mahamadou ya bayyana cewa, Nijer da Sin suna more kyakkyawar abokantaka da muhimmiyar hadin gwiwarsu a fannonin samar da kayayyakin more rayuwa, da albarkatun mai, da kiwon lafiya, da ilmi da sauran fannoni, wanda yake matukar amfanawa kasashen biyu da al’ummunsu. Nijer tana dora muhimmanci wajen karfafa huldar dake tsakaninta da kasar Sin, kana tana burin yin aiki tare da Sin don ingiza dangantaka abokai da muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakaninsu zuwa sabon matsayi. (Ahmad Fagam)