logo

HAUSA

Sin: Siyasantar da wasannin motsa jiki ya saba wa ruhin Olympics

2021-11-19 19:50:01 CRI

Sin: Siyasantar da wasannin motsa jiki ya saba wa ruhin Olympics_fororder_olympics-2022

A cewar wasu rahotanni, shugaban kasar Amurka Biden ya tabbatar da cewa, yana tunanin "kauracewa gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing a diflomasiyance. Dangane da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, siyasantar da wasannin motsa jiki ya sabawa tsarin wasannin Olympics, kuma yana cutar da muradun 'yan wasa daga dukkan kasashen duniya. Batun Xinjiang harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kuma ba za a lamunci makiyan kasar Sin daga waje su tsoma baki ta kowace fuska ko hanya ba.(Ibrahim)