logo

HAUSA

Ba a samu hare-haren ta’addanci ba a jihar Xinjiang cikin shekaru biyar a jere

2021-11-18 11:34:02 CRI

Ba a samu hare-haren ta’addanci ba a jihar Xinjiang cikin shekaru biyar a jere_fororder_201391875544997419

A jiya Laraba, kakakin gwamnatin jihar Xinjiang ta kasar Sin, Mr. Xu Guixiang ya bayyana a birnin Beijing cewa, cikin ’yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakan na yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, wadanda suka dakile yawan aukuwar hare-haren ta’addanci a jihar ta Xinjiang, wanda hakan ya sa ba a samu hare-haren ta’addanci ba a jihar cikin shekaru biyar a jere, matakin da ya kasance babbar gudummawar da kasar Sin ta bayar a fannin yaki da ta’addanci a fadin duniya.

Xu Guixiang ya ce, cikin ’yan shekarun da suka gabata, jihar Xinjiang na matukar mai da hankali a kan kyautata rayuwar al’umma, inda ta ware sama da kaso 70% na kudinta ga kyautata rayuwar al’umma cikin shekaru da dama a jere, don aiwatar da jerin ayyuka na samar da guraben aikin yi da kyautata rayuwar al’umma. Ya ce,“Dukkanin al’umma da ke fama da talauci da yawansu ya kai kimanin miliyan 3.06, sun fito daga kangin talauci, har ma an kai ga daidaita matsalar talauci da aka dade ake fuskanta a yankin. Yanzu haka al’umma ’yan kabilu daban daban na jihar na zaman walwala, lamarin da kuma ya kara inganta tushen aikin yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a yankin.” (Lubabatu)