logo

HAUSA

Mataimakin shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin gina tattalin arzikin duniya

2021-11-18 11:00:56 CRI

Mataimakin shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin gina tattalin arzikin duniya_fororder_a02-Chinese VP stresses importance of building open world economy

Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da bude kofarta tare da samar da karin damammaki ga duniya da kuma bayar da gudunmawa wajen gina tattalin arzikin duniya.

Wang ya yi wannan tsokaci ne cikin muhimmin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo yayin bude taron dandalin bunkasa tattalin arziki na zamani na Bloomberg na shekarar 2021.

A yayin da ake fama da annobar COVID-19, da kuma manyan sauye-sauyen da duniya ke fuskanta a halin yanzu, kasar Sin ta tsaida kudirin zurfafa manufarta na yin gyare gyare a gida da bude kofa mafi girma ga duniya da kuma nacewa kan aniyarta na gina ci gaban duniya.

A cikin jawabin nasa, Wang ya yi kira ga kasashen duniya da su daga matsayin harkokin cinikayya da saukaka hanyoyin zuba jari, kana su magance matsalolin gibin da ake samu da koma bayan cigaba.

Wang ya ce, ya kamata a yi hadin gwiwa da juna wajen ingiza amfani da hanyoyin bunkasa cigaba ba tare da gurbata muhalli ba da bunkasa kirkire kirkire, da rungumar hakikanin tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban, kana a taimaka wajen gina tsarin cigaba na bai daya wanda ke shafar salon cinikayyar bangarori daban daban. (Ahmad Fagam)