Hadin Kan Sin Da Amurka Zai Taimaka A Gudu Tare A Tsira Tare
2021-11-18 16:19:52 CRI
BY CRI HAUSA
Yayin zantawar da shugaba Xi Jinping na Sin da takwaransa na Amurka Joe Biden suka yi ta kafar bidiyo a ranar Talata, sassan biyu sun jaddada abun da masharhanta suka jima suna bayyanawa, don gane da muhimmancin hadin kan kasashen biyu, matakin da ake kallo a matsayin jigon cimma moriyar juna tsakanin kasashen biyu, da kuma zai haifarwa sauran sassan duniya karin alfanu.
Ko shakka babu, sanin kowa ne cewa Sin da Amurka, na jagorantar duniya a fannoni da dama, kasancewar su a sahun gaba ta fuskar karfin tattalin arziki, wanda ke ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. Kaza lika hadin gwiwar su zai ci gaba da share fagen tunkarar kalubalolin da duniya ke fuskanta a matakin shiyya shiyya da na kasa da kasa.
To amma kuma duk da haka, kasashen biyu ba za su kai ga baiwa duniya wannan cikakken zarafi ba, har sai sun kawar da banbance banbance dake tsakanin su, sun martaba juna, tare da rungumar manufofin cin gajiyar juna, da kaucewa yin fito na fito da ka iya illata moriyar su da sauran duniya baki daya.
A dukkanin tattaunawar shugabannin biyu, sun jaddada muhimmancin rungumar juna, da fatan yin aiki kafada da kafada wajen inganta huldar su yadda ya kamata. A hannu guda, shugaban Amurka ya sake nanata kudurin Amurka na biyayya ga manufar nan ta amincewa da kasar Sin daya tak a duniya, wanda hakan ya sabawa kalaman da wasu jami’an Amurka suka sha yi, cewa wai Amurkan na fatan tabbatarwa yankin Taiwan na Sin damar samun kariya.
To amma fa sai dai a nan, akwai bukatar “A gani a kasa, wai an ce da kare ana biki a gidan ku”! Ko shakka babu, kalaman shugaba Biden a yayin ganawarsa da shugaba Xi a farkon mako, za su zamo gaskiya ne kadai, idan har kasar sa, da jami’an gwamnatin ta suka dakatar da aiwatar da matakai na zahiri, masu nuni ga yiwuwar kulla wata huldar kashin kai da yankin Tawai, suka kuma dakatar da furta kalamai masu harshen damo, daka iya gurgunta yarda tsakanin Amurka da bangaren Sin.
Daga karshe, kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana, daya daga abubuwa mafiya muhimmanci da za su faru don gane da huldar kasa da kasa a shekaru 50 masu zuwa, shi ne gano yadda Sin da Amurka za su yi tafiya tare cikin lumana. A wani yanayi na “A guda tare a tsira tare”.