logo

HAUSA

Masu ruwa da tsaki na kira da a tallafawa kwallon kafa a Afghanistan

2021-11-18 20:30:09 CRI

Masu ruwa da tsaki na kira da a tallafawa kwallon kafa a Afghanistan_fororder_1118-1

Joyful Hashmatullah, mazaunin birnin Kabul na Afghanistan ne, wanda kuma ke sha’awar buga kwallon kafa, a yanzu haka kuma yana kira ga matasa ‘yan uwansa dake kasar, da su shiga harkar wasan kwallon kafa, tare da mara baya ga kulaflikan kwallon kafa dake kasar.

Joyful Hashmatullah mai shekaru 27 da haihuwa, ya ce yana farin cikin ganin a yanzu zai iya kallon wasan kwallo cikin kwanciyar hankali a birnin Kabul.

A baya bayan nan ne aka bude gasar kwallon kafar kulaflikan Afghanistan, gasar da ta kunshi kungiyoyin kwallon kasar daga larduna daban daban, kuma wannan ne karon farko da aka bude irin wannan gasa a Afghanistan, tun bayan da Taliban ta sake karbe iko da Kabul a ranar 15 ga watan Agustan da ya gabata, ta kuma kafa gwamnatin rikon kwarya.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin larabai na Xinhua, mashiryin gasar Arjumand Lali ya ce "Abu ne mai faranta ran mu, ganin yadda za a kaddamar da gasar kwallon kafa, bayan sauyin siyasa da kafuwar sabuwar gwamnati cikin lumana".

Lali ya ce ya yi imanin gudanar da gasanni musamman irin na kwallon kafa, za su samarwa al’ummar kasar farin ciki da nishadi da hadin kai, don haka ya yi kira ga ‘yan Afghanistan da su halarci wasannin gasa, su kuma goyawa ‘yan wasan kungiyoyin kasar baya, yayin da ake taka leda.

An dai sanyawa gasar ta kwanaki 8 sunan "Gasar zaman lafiya". To sai dai kuma, gasar ta bana ba ta samu masu daukar nauyi ba, in banda hukumar kwallon kafar kasar, kamar dai yadda Lali ya bayyana.

Shi kuwa Mohammad Khalid, wanda ke goyon bayan kungiyar Miwand Atalan, shaidawa Xinhua ya yi cewa, yana ganin kungiyar da yake goyon baya za ta samu nasara kan takwararta ta Shaheen Asmaee.

Khalid wanda ya isa birnin Kabul daga lardin Kandahar na kudancin kasar, domin ganewa idanunsa yadda gasar za ta gudana, ya ce yana fatan ganin karin masu kallo suna shiga filayen da ake gudanar da gasar.

Masu ruwa da tsaki na kira da a tallafawa kwallon kafa a Afghanistan_fororder_1118-2

Tun daga shekarar 2012 da aka fara buga wannan gasa, mata da ‘yan matan Afghanistan na cikin masu zuwa domin goyawa kungiyoyin kwallon kafar dake taka leda baya.

A cewar wani dan wasan kwallon kafa, Sanahullah Mohmand "Ina fatan ganin karin masu kallon wasa, da masu goya baya ga kungiyoyin kwallon kafa, su rika shiga kallon wasannin mu.

A karshen makon jiya a kalla ‘yan kallo 200 ne suka shiga filin buga kwallo, domin kallon gasar dake gudana. To sai dai kuma, Mohmand ya nuna rashin gamsuwa bisa karancin adadin, yana mai cewa, fatan sa shi ne ganin dubban mutane ‘yan kallo.

Gasar kwallon kafar kulaflikan Afghanistan na zuwa ne a gabar da kasar ke fuskantar halin rashin tabbas a fannin siyasar kasar, da matsalar talauci, da raunin tattalin arziki da suka dabaibaye sabuwar gwamnatin Taliban, wadda kawo yanzu ke kokarin samun karbuwa daga sassan kasa da kasa, bayan da Amurka ta daskarar da asusun kasar mai kunshe da kudin da yawan su ya kai har dalar Amurka biliyan 10.

To sai dai duk da haka, kakakin kwamitin shirya gasar Olympic a Afghanistan Dad Mohammad Nawak, ya tabbatar da cewa, sabuwar gwamnatin kasar za ta ci gaba da taimakawa harkar wasanni, da ‘yan wasan motsa jiki yadda ya kamata.