logo

HAUSA

Adadin mutanen da suka mutu a harin Burkina Faso ya karu zuwa 53

2021-11-18 10:14:41 CRI

Adadin mutanen da suka mutu a harin Burkina Faso ya karu zuwa 53_fororder_A01-Death toll from attack rises to 53 in Burkina Faso

Yawan mutanen da suka mutu a harin ranar Lahadi da aka kai arewacin kasar Burkina Faso ya karu daga mutane 32 zuwa 53, wanda ya hada har da jami’an tsaro 49, ministan sadarwa na kasar kana kakakin gwamnatin kasar, Ousseni Tamboura ya tabbatar da hakan a taron majalisar ministocin kasar na ranar Laraba.

Ministan ya bayyana cewa, an kuma samu wasu jami’an tsaron gendarmes kimanin 46 da ransu.

A cewar majiyar gwamnatin, an sauke kwamandan runduna ta daya na shiyyar da kuma na rundunar tsaro ta shiyyar arewaci daga kan mukamansu.

Gwamantin kasar ta bayar da hutun kwanaki uku a matsayin ranaku makoki a fadin kasar don nuna juyayin mutanen da suka rasu a harin tun daga ranar Talata zuwa Alhamis.

Tun a shekarar 2015, kasar Burkina Faso take fuskantar tabarbarewar yayayin tsaro tare da samun munanan hare-hare wadanda suka yi sanadiyyar hasarar rayukan mutane sama da 1,000, da kuma raba wasu mutanen sama da miliyan guda da gidajensu. (Ahmad)