logo

HAUSA

Merkel ta ce ba daidai ba ne a raba gari da kasar Sin

2021-11-18 19:43:42 CRI

A baya-bayan nan ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa, ba daidai ba ne, a raba gari kwata-kwata da kasar Sin, wanda yin haka zai haifar da illa ga Jamus da ma Turai. A don haka ta ba da shawarar cewa, Jamus da kungiyar tarayyar Turai, su ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin.

Da yake mayar da martani ga kalaman Merkel a yau Alhamis, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi nuni da cewa, a zamanin da ake ciki na dunkulewar duniya, mutunta juna da samun nasara, su ne muhimman jigon dangantakar kasa da kasa.(Ibrahim)