logo

HAUSA

Taron kasa da kasa: Manufar Sin daya tak ta samu gagarumar amincewa a tsarin huldar kasa da kasa

2021-11-18 16:28:15 CRI

Taron kasa da kasa: Manufar Sin daya tak ta samu gagarumar amincewa a tsarin huldar kasa da kasa_fororder_2758

A wannan rana ta 18 ga watan Nuwamba, an gudanar da babban taron kasa da kasa game da muhimmancin kudiri mai lambar 2758 na taron kolin MDD. Tsoffin ‘yan siyasa, da jami’an diflomasiyya, da kwararru da masana daga kasashe da dama dake nahiyoyin Asiya, Turai, da Latin Amurka, sun gudanar da tattaunawa mai zurfi game da batun manufar kasar Sin daya tak a duniya wanda aka tabbatar da kudirin.

Mahalartan sun bayyana cewa, kudirin mai lambar 2758 ya tabbatar da cewa, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin ita ce kadai halastacciyar gwamnati dake wakiltar kasar Sin a matakin kasa da kasa. Manufar kasar Sin daya tak a duniya ita ce hakikanin tsarin dokar hulda ta kasa da kasa wanda aka amince da ita karkashin kudirin doka mai lambar 2758, kudurin da ya samu gagarumar amincewa daga al’ummar kasa da kasa kuma ba tare da nuna adawa ko kuma kalubalanta ba.(Ahmad)