logo

HAUSA

Xi ya ce Sin za ta ci gaba da inganta dangantakarta da Isra'ila

2021-11-17 20:33:27 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a Larabar nan cewa, kasarsa za ta yi amfani da bikin cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya tsakaninta da Isra'ila a shekara mai zuwa, a matsayin wata dama ta sa kaimi, wajen raya hadin gwiwarsu a fannin kirkire-kirkire cikin lumana da kwanciyar hankali.

A cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Isra'ila Isaac Herzog, Xi ya ce, kasar Sin tana mutunta dangantakarta da Isra'ila matuka, kuma a shirye take ta hada kai da bangaren Isra'ila don samar da karin moriya ga jama'arsu.(Ibrahim)